Bisa halin da ake ciki yanzu a kasar Sin dangane da kamuwa da cututtuka a wurin aiki, wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bayyana a kwanan baya cewa, nan gaba, za a ci gaba da inganta dokoki, da kafa tsarin sanya ido kan cututtuka da ake kamuwa a wurin aiki da na shawo kansu, sa'an nan za a kara kokari wajen sanya ido kan masana'antu don kiyaye lafiyar jikin 'yan kwadago.
Ya zuwa karshen shekarar bara, jimlar mahakan kwal da suka kamu da cututtuka a wurin aiki ta wuce dubu 670 a kasar Sin. Bisa kidayar da ma'aikatun kiwon lafiya na kasar Sin suka yi, an ce, wuraren aiki da ake kamuwa da cututtuka sun hada da mahakan kwal da masana'antun narke karfuna da na sarrafa magunguna da kera motoci da na'urori masu aiki da kwakwalwa da hada magungunan sha da sauran sabbin sana'o'i. Daga cikinsu, 'yan kwadago wadanda ke kamuwa da cututtuka a wurin aikin kwal su ne mafi yawa, sa'an nan kuma sai masana'antun narke karfuna da masana'antun yin kayayyakin gine-gine.
1 2 3
|