Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 15:48:30    
Mutanen kasar Sin sun fi so su je motsa jiki a lokacin hutu

cri

Shugabar kolejin koyon wasanni ta birnin Beijing madam Wang Kaizhen ta ce,mutane da yawa suna shan aiki ba su da lokaci su je motsa jiki,shi ya sa suke zuwa motsa jiki a lokacin hutu,ana iya cewa,al`adar nan ba ta da kyau,saboda ba bisa kimiyya ba,za su gaji sosai.Madam Wang Kaizhen ta ba da shawara cewa,ya fi kyau a fara motsa jiki a kai a kai,alal misali,mutane su je lambun shan iska su yi tafiye-tafiye cikin sauri ko gudu sannu a hankali ko su je hawa dutse.Ta ce: `Yawancin mutanen kasar Sin ba su saba da motsa jiki ba tukuna,amma yanzu dai,suna shan aiki sosai kuma suna fama da matsin lamba ta fannoni daban daban.Idan ba su motsa jiki ba cikin dogon lokaci,to,jikinsu ba zai kasance cikin koshin lafiya ba.Saboda haka,kamata ya yi su je motsa jiki.Sa`an nan kuma kowa ya zabi wata hanya mai dacewa`

Madam Wang Kaizhen tana ganin cewa,a takaice dai,mutane su je motsa jiki a lokacin hutu shi ne abu mai faranta ran mutane,saboda a lokacin hutu,ana da isashen lokaci,amma abu mafi muhimmanci shi ne mutanen dake aiki su je motsa jiki a kowace rana,wato ba za su je motsa jiki a lokacin hutu kawai.(Jamila Zhou)


1 2 3