Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 15:48:30    
Mutanen kasar Sin sun fi so su je motsa jiki a lokacin hutu

cri

Duk wadannan sun nuna mana cewa,a cikin `yan shekarun da suka shige,mazauna biranen kasar Sin sun riga sun canja ra`ayinsu wajen kashe kudi,wato suna kara mai da hankali kan lafiyar jikinsu.Kwararrun mutanen da abin ya shafa suna ganin cewa,wannan yana da babbar ma`ana,ya nuna mana cewa,wasu mutanen kasar Sin suna yin kokari domin jin dadin zaman rayuwa mai inganci.

Duk da haka,wasu mazauna biranen kasar Sin ba su saba da motsa jiki ba,bisa sakamakon da aka samu bayan da aka yi wani bincike,an ce,mutanen kasar Sin kashi 40 cikin dari ne kawai suke motsa jiki,kuma yawancinsu su dalibai ne da tsofaffi wadanda suka riga suka yi ritaya daga aiki,samarin dake aiki ba su da yawa.Abu mai ban sha`awa shi ne wadannan samari sun fi so su je motsa jiki a lokacin hutu.Kwararrun mutane sun yi nuni da cewa,ba mai iyuwa ba ne a kyautata lafiyar jiki ta hanyar motsa jiki a cikin gajeren lokaci,balle ma a cikin kwanaki bakwai.


1 2 3