Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 15:48:30    
Mutanen kasar Sin sun fi so su je motsa jiki a lokacin hutu

cri

Kamar yadda kuka sani,daga ran 1 zuwa ran 7 ga watan Mayu na kowace shekara,a kullum mutanen kasar Sin suna jin dadin dogon lokacin hutu wato za su huta da kwanaki bakwai.Amma a cikin shekaru 2 da suka shige,a cikin wadannan kwanaki bakwai,Yang Kai,manajan sashen sayar da kayayyakin motsa jiki na kasuwar Huatang ta birnin Beijing wanda ke sauka a titin zhanlan yana shan aiki sosai,a shekarar bana kuma,shi ma yana shan aiki.Mr.Yang Kai ya ce,dalilin da ya sa haka shi ne domin mutane da yawan gaske sun kan je kasuwarsa domin sayen kayayyakin motsa jiki.

Mr.Yang Kai ya bayyana cewa,daga ran 1 zuwa ran 7 ga watan Mayu na shekarar bara,yawan kudin da kasuwar Huatang ta samu daga wajen sayar da kayayyakin motsa jiki ya karu da kudin Renminbi yuan fiye da dubu dari daya idan an kwatanta shi da kudin da kasuwar nan ta saba samu a kowane mako.A shekarar da muke ciki,ko shakka babu za a ci gaba da samun irin wannan sakamako.Ya ce:  `Daga fasahohin da muka samu,lallai mun sayar da kayayyakin motsa jiki da yawa.Alal misali,samari su kan sayi tufafin motsa jiki da takalman motsa jiki,saboda ba su da tsada.Game da sauran kayayyakin motsa jiki kamarsu kayayyakin wasan kwallon tennis da kayayyakin wasan hawan dutse da sauransu,yawancin masu sayensu su samari ne dake aiki a kamfanonin kasashen waje.Wadannan samari su kan sha aiki wato ba su da lokacin hutu da yawa,idan sun samu lokaci,sun fi so su je motsa jiki.Abu mai faranta ran mutane shi ne a kullum muna sayar da kayayyakin motsa jiki da yawa.`

Mr.Xiong Gang yana aiki a wani kamfanin kasar waje,ya riga ya saba da motsa jiki,kuma ya sayi katin motsa jiki na kulob na motsa jiki.Ya bayyana cewa,makasudinsa shi ne don kara lafiyar jikinsa,amma a cikin kwanaki bakwai na hutu,mutane da yawan gaske za su shiga kulob na motsa jiki domin motsa jiki,ba shi son irin wannan hali.Ya ce:  `Na fara motsa jiki kafin shekaru uku da suka shige,ba na son kashe kudi kan wasa da abinci kawai,na fi son kashe kudi don kyautata lafiyar jikina,amma ba na son lokacin hutu saboda mutane da yawan gaske za su zo motsa jiki tare da ni,kulob ba shi da isashen malaman koyar da wasa,ba na jin dadi.`


1 2 3