Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 17:47:55    
Kasar Sin tana kokartawa wajen inganta hadin kanta da kasashen duniya a fannin yawan mutane

cri

Ba ma kawai matsalar yawan mutane wata matsala ce da kasar Sin ke fuskanta ba, har ma sauran kasashen duniya musamman dimbin kasashe masu tasowa su ma suna fuskantar irin wannan matsala. Malam Zhang Weiqing ya kara da cewa, a sakamakon daga matsayin bunkasuwar harkokin tattalin arzikin kasar Sin da zamantakewar jama'arta, kasar Sin ita ma ta fara ba da gudummowa ga sauran kasashe a fannin yawan mutane. Ya ce, "kasar Sin ta dauki wani sabon mataki wajen hadin kanta da kasashen duniya a fannin yawan jama'a da bunkasuwa. Kuma tana canja hanyar da take bi wajen samun babbar gudummowa daga kasashen waje don ta zama hanyar da take ci gaba da samun gudummowar da ba da gudummowa ga kasashen waje, ta yadda za a sa kaimi ga gamayyar kasa da kasa su cim ma manufar zaman tare da cin nasara gaba daya."

Malam Zhang Weiqing ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta yi duk abubuwa da take iya yi wajen kara ba da taimako ga kasashe masu tasowa. Ya ce, kasar Sin ta shigar da hadin guiwa a tsakaninta da kasashen Afrika a fannin yin haihuwa lami lafiya da kayyade haihuwa cikin tsarin hadin guiwa na aiwatar da shirin aiki na nan gaba na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ya zuwa shekarar 2010, kasar Sin za ta horar da jami'ai da kwararru 300 da abin shafa domin kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika. (Halilu)


1 2 3