Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 17:47:55    
Kasar Sin tana kokartawa wajen inganta hadin kanta da kasashen duniya a fannin yawan mutane

cri

A gun wani taro da aka shirya a kwanakin baya, Malam Zhang Weiqing, babban direktan hukumar kula da yawan mutane da kayyade haihuwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa bisa matsayinta na wata babbar kasa wadda ke sauke nauyi a kanta, za ta yi kokari sosai wajen inganta hadin kan kasa da kasa a fannin yawan mutane, don ba da babban taimako wajen bunkasa harkokin yawan mutane a duniya.

Kasar Sin wata babbar kasa ce mai yawan mutane biliyan 1.3. Harkokin kula da yawan mutane da kayyade haihuwa da ake yi a kasar Sin suna kawo babban tasiri ga kasar, kuma ga bunkasuwar duniya. Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar kayyade haihuwa a shekarun 1970, yawan yara da aka haifa ya ragu da sama da miliyan 400 a cikin shekaru 30 da 'yan doriya da suka wuce. Ta haka, an sassauta matsin lamba da karuwar yawan mutane ke yi wa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da albarkatun kasa da kuma muhalli.


1 2 3