Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 17:47:55    
Kasar Sin tana kokartawa wajen inganta hadin kanta da kasashen duniya a fannin yawan mutane

cri

Malam Zhang Weiqing ya kara da cewa, "kasar Sin ta aiwatar da ayyukan asusun kula da yawan jama'a na majalisar dinkin duniya kamar yadda ya kamata. Ta hada kanta da asusun kula da yawan jama'a na majalisar dinkin duniya da gidauniyar Ford don gudanar da ayyukan kayyade haihuwa da hidimar haihuwa da kyau, da sa kaimi ga yin amfani da ra'ayoyi da sakamako mai kyau da kasashe daban daban suka samu. Ta haka an kyautata hanyoyi da kasar Sin ke bi wajen yin ayyukan kula da yawan jama'a da kayyade haihuwa."

Ban da kungiyoyin kasa da kasa, gwamnatin kasar Sin ta sami sakamako mai kyau wajen yin hadin guiwa a tsakaninta da na kasashen Japan da Australiya da sauransu a fannin kula da yawan jama'a. Malam Zhang Weiqing ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta kara gudanar da ayyuka cikin hadin guiwarta da sauran kasashen duniya, za ta ci gaba da yin ayyukan hadin guiwa a tsakaninta da asusun kula da yawan jama'a na majalisar dinkin duniya da gwamnatocin kasashen Japan da Australiya da kuma kungiyoyin kasa da kasa.


1 2 3