Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-20 15:59:59    
Masana'antun gida da na waje suna fuskantar haraji bai daya da ake bugawa a kansu a kasar Sin cikin amincewa

cri

Malam Yamashita Toshio ya ci gaba da cewa, "bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO, ta kara bude wa kasashen waje kasuwanninta, duk kyawawan manyan masana'antun duniya suna son yin takara a kasar Sin. Muna farin ciki da ganin takara da ake yi tsakanin duk masana'antu cikin daidaici. Fitar da kayayyaki da ake bukata a kasuwannin kasar Sin ya fi muhimmanci. Sabo da haka a ganina, irin wannan haraji bai daya da kasar Sin za ta buga ba zai kawo barazana ga masana'antu da 'yan kasuwa na kasashen waje suka kafa a kasar ba. "

A sakamakon ci gaba da ake samu wajen raya kasar Sin, tsarin haraji da kasar Sin ke bugawa a kan masana'antun gida da na waje ba ya iya dacewa da halin da ake ciki ba. Sabo da haka masana'antun gida sun nemi da a soke yawan haraji ba iri daya ba da ake bugawa a kan kudin shiga da masana'antun gida da na waje ke samu. Malam Li Dongsheng, babban direktan shahararren masana'antun yin kayayyakin gida masu aiki da wutar lantarki na kasar Sin yana ganin cewa, "haraji bai daya da za a buga a kan masana'antu yana dacewa da halin da ake ciki sosai. Bangaren masana'antun sun dade suna kira da a yi haka. Yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya kai wani babban mataki. Bayan da ta shiga kungiyar WTO, kasar Sin ta soke manufofinta da dama dangane da bai wa masana'antun 'yan kasuwa na kasashen waje iznin sayar da kayayyaki a kasuwanni da sauran abubuwa da ake kayyadde musu. Don haka harajin bai daya da za a buga yana da gaskiya. "(Halilu)


1 2 3