Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-20 15:59:59    
Masana'antun gida da na waje suna fuskantar haraji bai daya da ake bugawa a kansu a kasar Sin cikin amincewa

cri

Malam Yamashita Toshio, babban manajan kamfanin Omron a kasar Sin ya bayyana cewa, mun riga mun shirya sosai wajen fuskatar sabon tsarin haraji da za a buga a kan kudin shiga da masana'antun ke samu, ya ce, "a ganina, wannan doka da kasar Sin ta kafa ba za ta kawo tasiri ko kiris ga harkokin zuba jari da muke yi a kasar Sin a halin yanzu ba. Mu iya cewa, gwamnatin kasar Sin tana kara kawar da bambanci da ake nunawa a tsakanin masana'antun gida da na waje sannu a hankali, wannan mataki da ya kamata kasar Sin ta dauka bayan da ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. A hakika dai, tun daga ranar da kasar Sin ta shiga kungiyar, sai an iya hasashe cewa, gwamnatin kasar Sin za ta rage gatanci da take nuna wa masana'antun waje sannu da hankali. Amma wannan ba zai hana mu nuna amincewa ga zuba jari da muke yi a kasar Sin ba."

Malam Yamashita Toshio ya kara da cewa, kamfaninsa yana dora muhimmanci sosai ga kasuwannin kasar Sin. Yawan kudin jari da kamfaninsa ya zuba a kasar Sin ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 2 a cikin shekarun nan uku da suka wuce. Bisa shirinsa, Kamfanin OMRON zai sami dalar Amurka sama da miliyan 1,300 wajen sayar da kayayyakinsa a kasar Sin cikin shekarar nan, yawan kudin nan zai dauki kashi 20 cikin dari bisa duk kudin da yake samu.


1 2 3