A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka rufe shi a kwanakin baya, an zartas da "dokar haraji kan kudin riba na masana'antu bisa kuri'un amincewa masu rinjaye. A karkashin dokar, za a buga haraji bai daya a kan masana'antun gida da masana'antu da aka kafa bisa jarin kasashen waje a kasar Sin, yawan harajin zai kai kashi 25 cikin dari. Ta haka an daina nuna wa masana'antu masu jarin waje gatanci a fannin harajin, sa'an nan an kara samar da kyawawan gurabe ga masana'antun gida cikin adalci domin yin takara a kasuwanni.
Kasar Japan kasa ce ta biyu a girma a duk kasashe da ke zuba jari a kasar Sin. Ya zuwa yanzu, yawan kudin jari da kasar Japan ta zuba a kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 60, yawancin kamfanonin kere-kere na kasar Japan sun kafa sansanoninsu a kasar Sin. Babban kamfani mai suna Omron yana daya daga cikinsu, ya shahara a duk duniya wajen fitar da kayayyaki masu aiki da kansu da kayayyaki masu aiki da lantarki. Yanzu, yawan kudin jari da kamfanin ya zuba a kasar Sin ya kai miliyan darurruka.
1 2 3
|