'Suna wasa ne a cikin ruwa. Kananan kifaye da yawa suna zama a cikin tabkin, idan ka tsaya ko kuma ka kwanta a cikin ruwa ba tare da motsi ba, to, irin wadannan kifaye su kan taru a kewayen kafafunka, su kan sumbaci yatsun kafafunka, hakan na da ban sha'awa sosai.'
Manyan duwatsu da ruwa mai tsabta da kyakkyawan muhalli a kwarin Zhangbu da ke tsakanin manyan duwatsu sun samar da sharudda masu kyau ga tsire-tsire. Ana iya ganin dogayen tsoffin itatuwa a ko ina a nan. Manya 2 daga cikinsu suna zama tare, a tsakaninsu kuma, akwai wani katon dutse. Wadannan itatuwa sun rungume shi, suna kasancewa kamar yadda iyaye suke runguman yaronsu. Sa'an nan kuma, wasu itatuwa sun bude ganyayensu a rana, amma a dare kuwa, sun rufe su, wannan yana da mamaki sosai, har ma ka yi tsammani cewa, suna da hankalin tunani.
A lokacin da masu yawon shakatawa suke yawo a kwarin Zhangbu da ke tsakanin manyan duwatsu, sun more idanunsu da wadannan duwatsu da ruwa da itatuwa masu ban mamaki, wadanda ba safai a kan ga irinsu a sauran wurare ba, haka kuma, sun iya sauraran wakokin gargajiya masu dadin ji lokaci-lokaci. Dukkansu sun burge mutane kwarai.(Tasallah) 1 2 3
|