Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 16:57:06    
Ni'imtattun wurare masu ban mamaki a kwarin da ke tsakanin manyan duwatsu mai suna Zhangbu a Guizhou

cri

A bayyane ne wakilinmu ya ga wasu zane-zanen kalomimin Sinanci a kan manyan duwatsun, wasu sun zama wata jimla, wasu kuma sun yi kama da Turanci da Larabci. Bayan da masana masu ilmin sanin ma'adinai 10 ko fiye na kasar Sin sun yi nazarin wadannan duwatsu 2 masu ban mamaki, sun cimma amincewa da cewa, wadannan kattan duwatsu sun bullo ne saboda dalilin halitta, an gano wadannan zane-zanen kalmomi ne yau da shekaru sama da miliyan dari 2 da suka shige.

Wani shehun malami mai suna Li Tingdong yana ganin cewa, yiwuwar fitowar zane-zanen kalmomin a kan wani dutse domin dalilin halitta ta yi kadan ne sosai, ko kusa bai yiwu ba a fito da kalmomin Sinanci a kan duwatsu domin dalilin halitta a cikin kwarin Zhangbu. Shi ya sa ko shakka babu an mayar da wadannan duwatsu 2 tamkar abubuwan mamaki a duk duniya.

Duwatsun da aka samu kalmomin Sinanci a kansu sun jawo masu yawon shakatawa da yawa. Malam Bi ya je wajen ne don kallon wadannan duwatsu 2 masu ban mamaki, ya ce,

'A ganina, wadannan kalmomi da aka samu a kan duwatsun 2 ikon Allah ne, ba abubuwan duniyarmu ba ne.'

A zahiri kuma, a wurin shakatawa na kwarin Zhangbu da ke tsakanin manyan duwatsun, akwai duwatsu masu ban mamaki da yawa, kamar yadda duwatsun 2 da aka sami kalmomi a kansu.

A kusa da gabar kogin, akwai wani tabki, inda ruwa yake gangara sannu sannu, har ma ya kasance kamar yana hutu, ya yi kama da wani babban gilas da aka sa a kasa. A bakin tabkin, wasu budurwoyi na wurin sun sa kafafunsu a cikin ruwa, suna tsayawa ba tare da motsi ba, jim kadan wasu mutane suna kewayen wannan tabki, suna kallonsu. Madam Li Ya, mai jagorar masu yawon shakatawa ta gaya mana cewa,


1 2 3