Kwarin Zhangbu da ke tsakanin manyan duwatsu na cikin kudancin gundumar Pingtang, tsawonsa ya kai misalin kilomita 8 gaba daya. Da zarar shiga kwarin, sai a ga kyawawan wurare masu ni'ima. Kogin Zhangbu yana gangara ne a cikin kwarin da ke tsakanin manyan duwatsun, ruwan na da tsabta sosai har ma ya yi kama da wani madubi. A cikin kwarin, tsire-tsire kwarra suna girma sosai, kwazazzabo kuwa suna da tsayi ainun.
Duwatsun da aka samu a cikin kwarin Zhangbu su kan ba mutane mamaki, a cikinsu kuma manyan duwatsu 2 sun fi shahara. Bayan da ka shiga cikin kwarin har da nisan misalin kilomita dubu 2, sai ka ga wadannan kattan duwatsu 2 a gindin dogayen itatuwa 2 masu tsayin mita 10 ko fiye, su ne duwatsun da aka sami kalmomi a kansu. Wani manomi na wurin mai suna Wang Guofu ne ya tono wadannan duwatsu 2, ya waiwayi abubuwan da suka faru a lokacin can, ya ce,
'A watan Yuni na shekara ta 2002, na shige ta wannan wuri, ina tsammani cewa, akwai wasu kalmomi a kan wadannan duwatsu 2, a lokacin can na dudduba su a tsanake, ashe, su ne kalmomin Sinanci.'
1 2 3
|