Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-16 16:48:59    
Me ya sa ganawa ba ta shaifi batu mai muhimmanci

cri

Babu tantama ganawa a birnin kudus ba ta shafi muhimman batutuwa ba wannnanyana da nasaba da matakin da Abbas ya dauka. Kafofin yada labarai sun gane abin da mabiyansa suka furta kafin Abbas ya je birnin kudus cewa muhimman batutuwa da za su tattauna a wannan karo a yanzu su ne tsaro da taimakon tattalin arziki.Tun lokacin da aka kafa gwamnatin hadin kan al'umma ta Falastinu,kasashen Yamma ba su maido taimako ga gwamnatin Falastinu kai tsaye ba saboda kundin tsarin tafiyar da mulki nata bai biya muhimmin butaku na bangarori hudu da batun gabas ta tsakiya suka gabatar ba,zaman Falastinawa na kara tsamari,an sha samun yajin aiki saboda rashin biya albashi cikin dogon lokaci .Ban da wannan kuma har wa yau dai a kan samu tashin hankula tsakanin al'umman Falastinawa su kansu tun da aka kafa gwamnatin hadin kan al'umma.Ganin haka Abbas na bukatar Isra'ila da ta ba da hadin kai domin sassanta rikicin dake kasancewa a yanzu.Da ganin haka, Isra'ila da Falastinu ba su so su bata lokaci wajen tattauna muhimman batutuwa da ba a san makomarsu ba tukuna,sai su mai da hankali wajen warware wasu takamamen matsaloli.A cikin tattauwa Abbas ya bayyana cewa za a jibge sojojin tsaro a zirin Gaza da kuma yankin kasa na tsakanin zirin Gaza da kasar Massar domin hana dakarun Falastinu su yi satar shiga da makamai daga Massar zuwa zirin Gaza da kuma hana su harba rokoki kan Bani Isr'ila.Olmert ya alkawarta za a rufe karin tasoshin bincike na soja a yammancin kogin Jordan da tsawaita lokacin bude kofar Karni dale zirin Gaza inda shiga da fici na kayayyaki ta yadda za a kawo sauki ga Falastinu wajen samar da kayayyaki da kuma samun kayayyakin agaji na jin kai.

Kan sakamakon ganawa tsakanin shugaban Isra'ila da Falastinu a birnin Kudus,wakili na farko a shawarwari na Falastinu Saeb Erekat ya ce wannan masomi ne.Tattaunawa sau daya ba za ta iya warware dukkan matsaloli ba.Duk da haka shi kansa da madam Eisin,kakakin Olmert suna dauka cewa wannan ganawa tana da ma'ana mai amfani,dalili kuwa shi ne ta taimakawa wajen shimfida amincewar juna tsakanin shugabanni na Isra'ila da Falastinu.(Ali)


1 2 3