A ran 15 ga wata firayim ministan Isra'ila Ehud Olmert da shugaban mulkin kan al'umma na Falstinu Mahmoud Abbas sun gana a birnin kudus wadda ita ce karo na farko tun da aka kafa tsarin ganawa lokaci lokaci a tsakaninsu.A cikin wannan ganawar sun tattauna batutuwa na tsaro da kara sassauci a zaman Falastinawa da sauransu,duk da haka ba ta shafi batutuwa masu muhimmanci ba kan mallkar birnin kudus da dawowar 'yan gudun hijjira da shata kan iyakar karshe.Me ya sa aka shiga wannan hali,
Dalili kuwa shi ne Olmert ba ya so a tattauna muhimman batutuwa.Kafin ganawa ya ce ba zai tattauna wadannan batutuwa da Abbas ba.A ganin manazartan al'amuran duniya,Olmert ya dauki wannan mataki ne ya yi la'akari da abubuwan da ke karkashin kasa :
1 2 3
|