Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-16 16:48:59    
Me ya sa ganawa ba ta shaifi batu mai muhimmanci

cri

Da farko kullum Isra'ila tana jadadda cewa muddin Falastinu ta amince sharuda guda uku da bangarori hudu da batun gabas ta tsakiya ya shafa suka gabatar,wato amincewa da kafuwar Isra'ila a matsayin kasa da yin watsi da kai hare hare da amincewar yarjejeniyar da aka cimmawa kan daidaito,Isra'ila za ta yiwu ta tattauna batutuwa masu muhimmanci na shata iyakar kasas tsakaninta da Falstinu da matsayin birnin kudus da 'yan gudun hijjira na Falastinu.Gwamnatin hadin kan al'umma da aka kafa a watan jiya a cikin kundin tsarinta na tafiyar da mulki ta cigaba da kin amincewa da Isra'ila,ta cigaba da daukar yin dagiya da mutanen Isra'ila da karfin tuwo tamkar halalen ikon Falastinawa.Cikin wannan hali,idan Olmert ya yarda ya tattauna muhimman batutuwa da Abbas,babu shakka wannan zai zama aron baki ga 'yan hamayyarsa wajen kirkiro rigima.

Na biyu,dalilin da ya sa Isra'ila ba ta so ta tattauna muhimman batutuwa da Falastinu shi ne batun nan ya shafi shawarar zaman lafiya ta Larabawa da ke jawo hankulan mutanen duniya a yanzu.A taron koli na kasashen kawancen larabawa a Riad da aka yi ran 28 ga watan jiya,an sake gabatar da wata shawarar zaman lafiya ta larabawa ta shekara ta 2002.Bayan taron,bangarorin da abin ya shafa sun gana,sannan sun sami wani ra'ayi cewa za a nada wata tawagar tabbatar da shawarwa a taron ministoci na kawancen kasashen Larabawa da za a yi ran 18 ga wata wadda za ta tattauna da Isra'ila.Ta hanyar yin takamamen ganawa da shawarwari za a cimma burin samun zaman lafiya da baiwa falastinawa yankunan kasa.A ganin gwamnatin Isra'ila akwai wani abu da ya cancanci a yi tunani a kai cikin wannan ra'ayi,domin ganawar ba ta shafi moriyar Falastiu kawai ba.Ko za a iya rike da wannan ra'ayi wannan ya dogara da tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falastinu.


1 2 3