
Malam Ma Heli, wakilin hukumar tsare-tsare da raya kasa ta majalisar dinkin duniya da ke wakilci a kasar Sin yana ganin cewa, "ta hanyar yin wannan aikin tabbatar da tsaron lafiyar haka kwal a kasar Sin, kasar za ta kara kwarewa wajen horar da ma'aikata da ke aiki a mahakan kwal, musamman ma a lardunan nan biyar da muka ambata a sama bisa gwaji. Kasar Sin za ta kyautata halin da ake ciki sosai dangane da kiyaye mahakan kwal a kasar Sin musamman ma na garuruwa da kauyukanta. "
An ruwaito cewa, nan da shekaru hudu masu zuwa, kasar Sin da hukumar tsare-tsare da raya kasa ta majalisar dinkin duniya za su zuba dalar Amurka sama da miliyan 14 don gudanar da wannan aikin tabbatar da zaman lafiyar mahakan kwal na kasar Sin, daga cikin yawan wannan kudi, dalar Amurka sama da biliyan 2 za a same su ne daga wannan hukumar majalisar dikin duniya, sauran kudin kuma hukumomin matakai daban daban da mahakan kwal na kasar Sin ne za su samar da su. (Halilu) 1 2 3
|