
A kwanakin baya, babbar hukumar sanya wa aikin samar da kayayyaki ido cikin kwanciyar hankali ta kasar Sin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar da hukumar tsare-tsare da raya kasa ta majalisar dinkin duniya sun hada kansu sun fara gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiyar hakon kwal a kasar Sin, ta haka za a kyautata halin zaman lafiya da ake ciki a mahakan kwal na kananan garuruwa da kauyuka, sa'an nan za a kyautata dokoki da manufofi dangane da sa kaimi ga yin aikin hako kwal cikin kwanciyar hankali.
Ana yin aikin tabbatar da zaman lafiyar hako kwal a kasar Sin ne, musamman a larduna biyar da suka hada da Anhui da Guizhou da Henan da Liaoning da kuma Shanxi. Yayin da ake yin wannan aiki, za a koyar wa mahakan kwal da iyalansu ilmin kare kansu, da ba da taimako ga mahakan kwal na garuruwa da kauyuka wajen daga matsayinsu na kula da harkokin mahakan kwal, da kuma kyautata dokoki kan zaman lafiyar mahakan kwal.
1 2 3
|