Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-02 18:43:53    
Sin da majalisar dinkin duniya sun hada kansu don daga matsayin hako kwal cikin kwanciyar hankali

cri

Kasar Sin kasa ce mafiya girma a fannin hako kwal da yin amfani da shi a duniya. Yawan kwal da ake amfani da su ya dauki wajen kashi 70 cikin dari bisa na duk makamashi da ake yin amfani da su a kasar Sin. Malam Peng Jianxun, mataimakin shugaban hukumar sanya wa mahakan kwal ido kan zaman lafiyarsu ta kasar Sin ya bayyana cewa, "a cikin 'yan shekarun baya, kasar Sin ta kafa dokoki da ka'idoji da dama dangane da zaman lafiyar mahakan kwal, ta kara kyautata tsarin sanya wa mahakan kwal ido kan zaman lafiyarsu, ta yi ayyukanta musamman domin inganta zaman lafiyar mahakan kwal, ta rufe mahakan kwal da haramtattun mahakan kwal da yawa wadanda ba su dace da aikin hako kwal cikin kwanciyar hankali ba, kuma ta yi kokari sosai wajen kawar da hadarin gas daga mahakan kwal, kuma ta sami sakamako mai kyau."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kwal da aka hako a kasar Sin ya karu daga tan miliyan 1,300 a karshen karni na 20 zuwa tan miliyan 2,300 a yanzu, sa'an nan yawan mahakan kwal da suka mutu a sanadiyar hadari ya ragu daga 7,000 a ko wace shekara na karshen karni na 20 zuwa sama da 4,000 a shekarar bara.

Madam Hu Yuhong, mataimakiyar shugabar cibiyar musanya da hadin guiwar Sin da kasashen waje ta babbar hukumar sanya ido kan zaman lafiyar aikin samar da kayayyaki ta kasar Sin ta ce, kasar Sin tana kokarin koyon hanyoyin zamani da kasashen waje ke bi wajen kula da tsaron lafiyar mahakan kwal don kara daga matsayinta na kula da tsaron lafiyar mahakan kwal, ta hanyar hadin kanta da hukumar tsare-tsare da raya kasa ta majalisar dinkin duniya da kasashen waje. Ta bayyana cewa, "mun yi bincike kan dokoki da ka'idoji da ksasahen waje suka kafa dangane da tsaron lafiyar mahakan kwal, mun gayyaci wasu kwararrun kasashen waje don bayyana mana ma'aunan kasashensu da kuma tsare-tsarensu dangane da tsaron lafiyar mahakwan kwal. Sa'an nan mun shirya wasu taron kara juna sani na kasa da kasa, mun yi koyi da sakamako da kwararu suka samu a fannoni daban daban. "


1 2 3