
Kuna sane da, cewa yawan mutanen wasu kasashe masu sukuni dake yin wasannin motsa jiki yakan dauki kashi 5O zuwa kashi 60 cikin kashi 100 bisa jimlar mutanensu. Bisa binciken da aka taba gudanar a shekarar 2000, an ce, yawan mutanen da suke yin wasannin motsa jiki na kasar Sin bai kai kashi 34 cikin kashi 100 ba. Mr. Xu Chuan ya fadi, cewa makasudinmu shi ne kokarin kara yawansa zuwa kashi 40 cikin 100 a shekarar 2010.
Abun da ya faranta ran mutane, shi ne yawan mutanen da ke sha'awar yin wasannin motsa jiki na kasar Sin sai kara karuwa yake a kowace rana saboda sukan samu lokuta da yawa bayan aiki, musamman ma a dogon lokacin hutu na bikin murnar 'yancin kasa da kuma bikin ma'aikata na duniya da dai sauran bukukuwa.
A karshe dai, Mr. Xu Chuan ya bayyana, cewa bisa shirin da aka tsara, an ce, babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin za ta shirya wasu muhimman gasannin motsa jiki bisa babban mataki a cikin duk fadin kasar. Wadannan gasanni sun hada da wasan hawan dutse, da wasan kwallon tebur, da wasan ninkaya, da wasan kwallon tennis, da tseren kwale-kwale da dai sauran makamantansu masu ban sha'awa. Mr. Xu Chuan ya kuma sanar da, cewa ana gudanar da wadannan gasanni ne kusan a kowane wata na shekarar da muke ciki. A sa'i daya kuma, babbar hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin tana himmantar da sassa daban-daban masu kula da harkokin wasannin motsa jiki na wurare duk kasar don su shirya wasannin motsa jiki a wuraren a wannan shekara.( Sani Wang ) 1 2 3
|