Sa'annan Mr. Xu Chuan ya yi nuni da, cewa babbar dawainiyar ayyukan wasannin motsa jiki na babbar hukumar kasar Sin, ita ce inganta lafiyar jikin jama'ar kasar ba wai yin aiki da kyau wajen tafiyar da ayyukan wasannin motsa jiki da kuma barin 'yan takarar wasanni su hawa kan dakalin karbar lambobin yabo na taron wasannin Olympic kawai ba. ' Yin horaswa ga kungiyoyin da za su shiga taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008', in ji shi, ' wani aiki ne mafi muhimmanci dake gaban babbar hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta duk kasar. Amma duk haka, babban nauyiin dake bisa kan babbar hukumar shi ne, kyautata ingancin jikunan jama'ar'.
Kan batun yin wasannin motsa jiki na dukan jama'a, kamata ya yi a kula da ma'anar wata dake cewa 'yawan mutanen dake yin wasannin motsa jiki', wato ke nan ana nufin wasu mutanen da sukan yi wasannin motsa jiki na tsawon rabin awa kuma sau uku a kowane mako. Wassu manazarta a fannin wasannin motsa jiki sun yi hasashe, cewa yawan mutanen da suke yin wasannin motsa jiki yana da nasaba sosai da matsayin bunkasuwar tattalin arziki da kuma zamantakewar al'ummar kasa. Ko da yake wasu sassan kula da harkokin wasannin motsa jiki na kasar Sin sukan sanya kokari matuka wajen janyo hankulan mutane mafi yawa ga shiga wasannin motsa jiki, amma duk da haka, ya kasance da babban gibi tsakanin kasar Sin da kasashe masu sukuni a fannin yawan mutanen da suke yin wasannin motsa jiki sakamakon kuntatawar matsayin yalwatuwar tattalin arzikin kasar. Daga nan dai, Mr. Xu Chuan ya lashi takobin samun karin mutanen da suke yin wasannin motsa jiki nan da 'yan shekaru masu zuwa ta hanyar yin amfani da kyakkyawanr yanayin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing.
1 2 3
|