An labarta, cewa Mr. Xu Chuan, mataimakin daraktan sashen kula da wasannin mota jiki na jama'a na babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya fayyace a gun taron da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya shirya kwanakin baya ba da jimawa ba, cewa a shekarar da muke ciki, babbar hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin za ta tayar da manyan harkokin wasannin motsa jiki a fannoni 65 a cikin gidan kasar dake da lakabin haka : ' Ana gudanar da wasannin motsa jiki na dukan jama'a tare da wasannin Olympic' domin sa kaimi ga karfafa lafiyar jikin jama'ar kasar da kuma kago kyakkyawan yanayi domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.
Mr. Xu Chuan ya jaddada, cewa shekarar 2007, muhimmiyar shekara ce ta share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. To, a wannan lokaci, gudanar da harkokin wasannin motsa jiki a cikin dukan jama'ar kasar da ake yi yanzu bisa babban mataki yana da amfani ga sa kaimi ga mutanen da'i'rori daban-daban na zamantakewar al'ummar kasar Sin da su kara mai da hankali kan wasannin motsa jiki da kuma taron wasannin Olympic ; Haka kuma yana da amfani ga dukan jama'ar kasar wajen tayar da babban tashen wasannin motsa jiki, ta yadda za a mayar da yunkurin share fage da na gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a matsayin wani yunkurin inganta lafiyar jikin jama'ar kasar.
1 2 3
|