
A gun cikakken zama na farko na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar Kasar Sin da aka yi a watan Satumba na shekara ta 1949,marigayi Mao Zedong ya ci zaben zama shugaban gwamnatin jama'a ta tsakiya ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.A lokacin farko na kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin,shi kansa da sauran shugabanni na kwmitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun ja ragamar jama'ar kasa wajen komada tattalin arzikin kasa da gyara tsarin mallakar gonakai tare da nasara,sun kuma danne wadanda suka yi adawa da juyin juya hali,sun tura sojoji masu sa kai zuwa Korea domin yin adawa da Amurka da ba da tallafi ga Korea,ban da wannan kuma sun yi kokarin inganta mulkin kasa da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali.A karshen shekara ta 1952,ya gabatar da wani babban tafarki ga jam'iyyar a lokacin rikon kwarya,ya kuma tsara ka'idoji da manufofi a jere domin kakkafa masana'antu na zaman gurguzu,gwamnati ta kawo canji ga ayyukan aikin gona da sana'ar hannu da kuma ayyukan masana'antu da ciniki na masu jarin hujja bisa hanyar zaman gurguzu.
A Shekara ta 1954,ya ba da jagora wajen tsara kundin tsarin mulkin kasa na farko,kuma aka zabe shi da ya zama shugaban Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin a gun taron wakilan jama'ar kasa baki daya na farko.A watan Fabrairu na shekara ta 1952,ya bayar da wani jawabi "kan daidaita matsaloli dangane da sabani tsakanin jama'a yadda ya kamata",ya ba da ra'ayinsa a kan cewa kamata ya yi a bambanta sabanin dake tsakanin jama'a da sabanin dake tsakanin jama'a da abokan gaba,ya maida daidaita sabanin dake tsakanin jama'a cikin ajandar harkokin siyasa na gwamnatin.
A shekara ta 1958,ba tare da dogon tunani ba ya yi yunkurin neman samun cigaba fiye da kima,da kuma kakkafa kungiyoyin noma na jama'a a kauyuka.A shekara ta 1966,ya aikata kuskuren ta da "juyin juya hali na al'adu",wannan ya kawo mummunan barna da hassara ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatinta a fannoni da yawa.A shekarun saba'in na karni da ya shige,ya bayar da ra'ayi na shata duniya gidaje uku wato Amurka da Rasha suna cikin gida na farko da sauran kasashe masu cigaban masana'antu suna cikin gida na biyu da kasashe matasa suna cikin gida na uku.Ya juya dangantaka dake tsakanin kasar Sin da Amurka,daga nan wani hali mai armashi ya bullo a harkokin waje na kasar Sin.A ran 9 ga watan Satumba na shekara ta 1976,mallam Mao Zedong ya rasu a birnin Beijing.Da ya ke marigayi shugaba Mao Zedong ya yi kuskure a karshen rayuwarsa,taimakon da ya baiwa juyin juya hali na kasar Sin ya fi yawa,kuma dauwamame ne,shi ne babban jagora na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da na mutanen kabilu dabam daban na kasar Sin.Tunanin Mao Zedong da aka samu a cikin yunkurin da Jam'iyyar da mutanen Sin suka yi tare,dukiya ce mafi daraja ga Jam'iyyar kuma tunanin jagora ne ga Jam'iyyar.(Ali) 1 2 3
|