
A watan Afril na shekara ta 1927,ya halarci taron wakilan kasa baki daya a karo na biyar na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,aka zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na kwamitin tsakiya,a watan Yuni ya zama sakatare na kwamitin Hunan na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.A gun taron ran bakwi ga watan Augusta na wannan shekara na Jam'iyyar ya gabatar da wani shahararren ra'ayinsa wato "daga bakin bindiga ake samun mulkin kasa",aka zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na ofishin siyasa na wucin gadi na kwamitin tsakiya.Bayan taron ya ta da tawaye na yanayin kaka a yankunan dab da iyaka da ke tsakanin lardin Hunan da lardin Jiangxi,daga baya ya ja ragamar rukunin masu bore zuwa yankin tsaunuka na Jinggangshan ya kafa sansanin juyin juya hali na kauyuka na farko.A shekara ta 1928,rukuninsa ya hada da rukunan masu bore da marigayi Zhu De da Chen Yi ke jagora,aka kafa rukuni na hudu na rundunar soja ta juyin juya hali na ma'aikata da manoma( ba da dadewa ba aka canza sunanta zuwa jar rundunar soja),ya zama wakilin Jam'iyyar kuma sakatare na kwamitin fagen daga.Tare da idon basira 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin wadanda marigayi Mao Zedong muhimmin wakilinta sun bude wata hanyar juyin juya hali na samun mulkin kasa da makami ta dabarar yi wa birane zobe daga kauyuka da kuma kwace birane daga bisani bisa halin da kasar Sin ke ciki a wannan lokaci.A shekara ta 1930 ya zama babban kwamishinan siyasa na rukunin farko na jar runduna soja.
A shekara ta 1931,ya zama shugaban gwamnatin tsakiya ta rikon kwarya ta Jamhuriyar Soviet ta kasar Sin.A watan Janairu na shekara ta 1933 aka zabe shi da ya zama dan ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin.Tun daga karshen shekara ta 1930,Shi kansa da mallam Zhu De sun ja ragamar rukunin farko na jar rundunar soja wajen murkushe "zobe" na karo na farko da na biyu da na uku da sojojin Jam'iyyar Kuomintang.Duk da haka aka tilasta shi da ya bar guraban shugabanci na jam'iyyar da rundunar soja bisa matsin lamba da masu tsatsaurn ra'ayi na jam'iyyar suka yi masa.A watan Oktoba na shekara ta 1934,rukunin farko na jar rundunar soja ya fara doguwar tafiya wato long march a turance bayan da ya sha hassara a cikin "zobe" a karo na biyar da aka yi masa.A hanyar doguwaar tafiya a gun taron Zongyi da aka yi a watan Janairu na shekara ta 1935,aka gyara kuskuren da masu tsatsauran ra'ayi na jam'iyyar suka yi aka tabbatar da matsayin shugabanci na marigayi Mao Zedong a cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin da rundunar soja.
Bayan daJar rundunar soja ta isa arewancin lardin Shanxi tare da nasara,a watan Disamba na shekara ta 1935,marigayi shugaba Mao Zedong ya bayar da wani rahoto kan dabarun yaki da mahara japannawa,a cikin rahotonsa ya gabatar da wata manufar kafa hadaddiyar kungiyar adawa da mahara Japannawa ta al'umma.Bayan da yakin adawa da mahara Japannawa ya barke a shekara ta 1937,kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wanda marigayi shugaba Mao ke wakilinsa ya nace ga bin ka'idar 'yancin kai cikin hadaddiyar kungiyar yin adawa da mahara Japannawa,ya yi kokarin ta da mutanen Sin da su yi yakin sari-ka noke bayan fagen yaki,ya kafa sansanoni da dama na yin adawa da mahara Japannawa da neman dimakuradiya.A watan Maris na shekara ta 1943,aka zabi marigayi Mao Zedong da ya zama shugaban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.A gun taron wakilan kasa baki daya a karo na bakwai na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka yi a shekara ta 1945,aka mai da tunanin Mao Zedong ya zama tunanin jagora ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.Daga cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na bakwai na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,yana kan kujerar shugaban kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin har zuwa rasuwarsa.Bayan yakin adawa da mahara Japannawa ya sami nasara,a watan Augusta na shekara ta 1945,Shi kansa ya je birnin Chongqing don tattaunawa,ya yi iyakar kokarinsa wajen neman zaman lafiya da shimfida dimakuradiya.A yanayin rani na shekara ta 1946,Jiang jeshi ya tayar da yakin basasa daga dukkan fannoni,marigayi shugaba Mao da sauran shugabanni na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun yi jagora a cikin babban yakin suncin jama'a,a shekara ta 1949,aka hamburar da mulki na Jam'iyyar Kuomintang.
1 2 3
|