
An haifi marigayi shugaba Mao Zedong ne a gundumar Xiangtan ta lardin Hunan ta kasar Sin a ran 26 ga watan Disamba na shekara ta 1893,ya rasu a ran 9 ga watan Satumba na shekara ta 1976.Yana daya daga cikin manyan shugabannin kasar Sin wadanda suka kafa Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin da Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin.Shi kuma dan Marksanci ne mai girima da kuma dan juyin juya hali ne da masani shiri da hasashe na talakawa.Tun yana yaro,ya fara karatunsa a makaranta mai zama kansa.
Bayan da aka ta da bore a birnin Wuchang a shekara ta 1911,ya shiga wata sabuwar rundunar soja ta lardin Hunan.Tsakanin shekara ta 1914 da ta 1918 yana karatu a makarantar horaswar mallamai ta farko ta lardin Hunan da ke birnin Changsha.A watan Afril na shekara ta 1918 ya hada kansa da abokinsa Cai Hesheng da sauran abokansa ya kafa kungiyar nazarin ilmin sabon dimakuradiya,ya kintsa 'yan kungiyar da su fasahohin da aka samu a cikin juyin juya hali na watan Oktoba na kasar Rasha,ya kokarta wajen samo hanyoyi da dabaru na kawo wani canji a kasar Sin.A yanayin hunturu na wannan shekara ya zo birnin Beijing,ya zama wani ma'aikaci a cikin dakin ajiye littattafai na jami'ar Beijing wanda marigayi Li Dazhao shi ne darektansa.A ran 4 ga watan Mayu na shekara ta 1919,tare da kwazo da himma ya shiga wani zanga zanga da da 'yan makarantu na birnin Beijing suka yi,ya kuma shirya wata mujjala "Sharhin Xiangjiang" domin yin adawa da mayaudara da kuma mulkin gargajiya.
Tun daga shekara ta 1921 bi da bi ya kafa kungiyar nazarin al'adu da kungiyar nazarin harkokin Rasha da kungiyar samari na zaman gurguzu da wata tawaga ta kwamsanci ta lardin Hunan.A watan Yuli na shekara ta 1921 ya halarci taro na farko na wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na kasa baki daya.A watan Augusta ya zama darekatan reshen Hunan na ma'aikatar kula da kwadago ta kasar Sin,ya ba da jagora ga ma'aikata wajen tafiyar da harkokinsu.A shekara ta 1922 ya zama sakatare na kwamitin Hunan na jama'iyyar Kwaminis ta Sin.A watan Yuni na shekara ta 1923 ya halarci taro na uku na wakilan dukan saka na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,an kuma zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na kwamitin zartaswa na tsakiya da kuma manban ofishin kwamitin tsakiya da sakare.Bayan da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta hada kanta da jam'Iyyar Kuomintang ta kasar Sin,bi da bi ya halarci taron wakilan kasa baki daya na farko da na biyu na Jam'iyyar Kuomintang,aka zabe shi mamba ba cikakke ba na kwamitin zartaswa na tsakiya.A shekara ta 1925 ya zama mukkadashin shugaba na ma'aikatar fadakar da jama'a ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kuomintang,ya kuma shirya wata" jaridar mako-mako ta siyasa" wadda ita ce mujjalar hukuma ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kuomintang.A shekara ta 1926 ya kafa wata makarantar horar da manoma a karo na shida,ya horar da manoma ginshikai wajen tafiyar da harkokinsu.A watan Nuwanba na wannan shekara ya zama sakatare na kwamitin kula da harkokin manoma na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.
1 2 3
|