Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-22 12:56:18    
Halin da ake ciki a Somali wajen kwanciyar hankali yana ta kara lalacewa

cri

Tun shekarar 1991 zuwa yanzu, kullum Somali tana cikin halin rashin doka da oda sakamakon hare-haren da 'yan tawaye suke kaiwa. A shekarar 2004, an kafa gwamnatin rikon kwarya a Kenya, kuma an koma da ita kasar Somali a shekarar 2005, amma sabo da rishin karfi, shi ya sa kullum gwamnatin rikon kwarya ta kasa karfin mallake duk kasar baki daya. A watan Yuni na shekarar da ta wuce, dakarun rukunonin addinai wato kungiyar kawancen kotunan Islama ta mamaye Mogadishu, hedkwatar kasar, daga baya kuma tana ta kara karfita har 'yan watanni, gwamnatin rikon kwarya ta ga tilas ne ta janye jikinta zuwa garin Baidos da ked a nisan kilomita 250 daga arewa maso yammacin birnin Mogadishu. A karshen watan Disamba na shekarar da ta wuce, kuma bisa taimakon da aka samu daga sojojin Habasha, sojojin Somali sun kwace ikon mulkin yawancin wuraren kasar ciki hard a Mogadishu, hedkwatar kasar, amma birbishin dakarun rukunonin addinai sun bayyana cewa, za su sanya wani "yakin sari ka noke irin na Iraki", wannan ya sa kasar Somali cikin halin yamutsi.

Yadda halin da ake ciki a Somali zai samu ci gaba ya zama abun da ya kara jawo hankulan kasashen duniya. (Umaru)


1 2 3