
A ran 21 ga wata, an yi dauki ba dadi a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somali, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 17. Wannan ya zama fada mafi tsanani da aka yi a birni Mogadishu tun bayan da aka kori dakarun rukunonin addinai na Somali, kuma ya kara tsananta halin rashin kwanciyar hankali da ake ciki a Somali.
A safiyar wannan rana, wata rundunar da ke hade da sojojin gwamnatin Somali da na Habasha sun yi maci zuwa shiyyar tsakiyar birnin Mogadishu inda suka ci karo da darurruwan dakaru wadanda suka rufe fuskokinsu, sassan 2 sun gwabza da juna. Bayan da aka kammala yakin, dakarun sun ja wata gawar sojan gwamnatin Somali da ta sojon Habasha sun ketare wasu tituna, kuma sun kona wadannan gawawwaki 2. Bisa kididdigar da asibitin da ke wurin ya yi an ce, zuwa yanzu wannan yakin da aka tayar ya riga ya yi sanadiyar mutawar a kalla mutane 7, yayin da mutane 10 suka ji rauni.
1 2 3
|