Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-22 12:56:18    
Halin da ake ciki a Somali wajen kwanciyar hankali yana ta kara lalacewa

cri

Cikin 'yan watannin da suka wuce, kusan a ce ana ta yin hare-hare a kowace rana a kasar Somali. A ran 11 ga wata, gwamnatin kasar ta taba sanar da wani shirin samun kwanciyar hankali cikin wata daya, amma ba a samu sakamako sosai wajen tabbatar da shirin ba. Abun musamman shi ne bayan da gwamnatin rikon kwarya ta Somali ta yarda da maida gwamnatinta zuwa Mogadishu, hedkwatar kasar a ran 12 ga wata, sai birnin Mogadishu ya shiga cikin hare-hare na sabon zagaye. A ran 13 ga wata, an samu wani hargitsi a Mogadishu wato an yi yunkurin bindige Mr. Abdullahi Yusuf, shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Somali, a cikin yakin an harba watar madafu masu bakin turmi har sau 6 kan fadar shugaban kasar da ke kudancin birnin Mogadishu, shugaba Yusuf ya yi sa'a ya kubuta da kansa daga hadari, amma fararen hula da ke zaune a kusa da fadar shugaban kasa sun sha bala'i, wato daya daga cikin su ya mutu, kuma mutane 3 sun ji rauni. Cikin 'yan kwanaki na bayan wannan rana har zuwa yanzu, an yi ta yin hare-hare a wurin, har mutane fiye da 10 sun mutu, yawancinsu fararen hula ne wadanda ba su ci ba su sha ba, har ma da yara. Ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, wadannan hare-haren an yi su ne duk domin gitta Katanga ga gwamnatin rikon kwarya wajen aikinta na koma da hedkwatar kasar. Mr. Hussein Mohamoud Hussein, kakakin shugaban kasar Somali ya bayyana cewa, masu tada farmaki sun yi nufin tabbatar da cewa, gwamnatin rikon kwarya ta kasa karfin sarrafa halin da ake ciki a hedkwatar kasar ta hanyar yin hare-hare.


1 2 3