Kasar Sin wata babbar kasa ce da ke fitar da makamashi da yin amfani da shi. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta hada kanta sosai da kasashen Gulf a fannin makamashi da sauranu. Yanzu, Sin da kasashen gulf sun riga sun fara aiwatar da tsarin tattaunawa kan makamashi, kuma suna yin shawarwari a kan yarjejeniyar cinikayya mara shinge. Madam Liu Xianghua, wakiliyar kasar Sin kuma tsohuwar jakadar kasar a Lebanon ta bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da yin tattaunawa da hadin kai a tsakaninta da kasashen gulf a fannin makamashi da na zaman lafiya. Ta ce, "za mu tattauna tare da kasashen kwamitin hadin kai na gulf da hada kansu don sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya a yankin kamar yadda ya kamata, da gabatar da kyawawan guraben siyasa ga aikin samar da makamashi cikin kwanciyar hankali, da ci gaba da sa kaimi ga yin ziyara a tsakanin hukumomi da kamfanoni na makamashi, da kiyaye muhalli da raya makamashi da yin amfani da shi. Za mu nace ga tsarin tattaunawa kan makamashi a tsakanin Sin da kwamitin, mu binciki sabuwar hanya da za a bi wajen hadin guiwar makamashi don taimakon juna. Kasar Sin tana fatan tare da kasashen kwamitin za su sa kaimi ga yin tattaunawa kan makamashi a tsakanin kasashe masu fitar da makamashi da kasashe masu yin amfani da shi, don kara fahimtar juna, da rage bambanci da ke tsakaninsu, da bunkasa kasuwannin makamashi na duk duniya kamar yadda ya kamata." (Halilu) 1 2 3
|