Kasar Japan kasa ce mafi girma da ke shigowa da gurbataccen man fetur daga yankin gulf. Kashi 75 cikin dari na gurbataccen man fetur tana shigowa da su ne daga yankin nan. Madam Yuriko Koike, mai ba da shawara kan harkokin tsaro ta firayim ministan kasar Japan ta jaddada kan muhimmacin hadin kan kasashen gulf a fannin makamashi.
Haka kuma yawan gurbataccen man fetur da gas da kasar Indiya ke samu daga yankin gulf ya dauki kashi 70 cikin dari. Sabo da haka yayin da Yashiwant Sinha, tsohon ministan harkokin waje na kasar ke yin jawabi a gun taron, ya jaddada muhimmacin zaman lafiyar yankin gulf da yanayin tsaron makamashi ga Indiya da sauran kasashe daban daban, kuma ya gabatar da shawara ga kasashen Asiya masu fitar da makamashi da amfaninsa su kafa tsarin tattaunawa kan yanayin tsaron makamashi cikin dogon lokaci. Ya ce, "ya kamata, manyan kasashen Asiya su rika yin tattaunawa a tsakaninsu da kaasahen gulf har cikin dogon lokaci. Mu iya kafa dandalin tattaunawa na yammacin Asiya daidai kamar na gabashin Asiya, don yin shawarwari a kan batun zaman lafiya da ke jawo hankulan kasashen yammacin Asiya, ta yadda za a gabatar da shirin daidaituwa."
1 2 3
|