Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 16:27:41    
Manyan kasashen Asiya masu fitar da makamashi da amfaninsa suna son hadin kansu a fannin makamashi

cri

Tun daga ran 19 zuwa ran 21 ga wata, a birnin Doha, hedkwatar kasar Qatar, an yi babban taro na biyu kan bunkasuwar tattalin arzikin gabas ta tsakiya nan gaba. Manyan kasashe masu fitar da makamashi da amfaninsa wadanda suka halarci taron sun gabatar da shawara kan kara yin tattaunawa ga harkokin tsaro, da inganta hadin kansu a fannin makamashi da tattalin arziki ta hanyoyi daban daban.

Manyan batutuwa da taron ya tattauna a kai sun hada da zaman lafiyar yankin gulf, da rawar da kasashen Asiya da yankin gabas ta tsakiya ke takawa, da kwarewar kasashen gabas ta tsakiya a fannin takara da sauransu. A gun taron, Sheikh Hamad Bin Jabor, babban sakataren hukumar tsare-tsare ta kasar Qatar da ke a yankin gabas ta tsakiya ya bayar da jawabi, inda ya jaddada yanayin tsaron makamashi da ci gaba mai dorewa da ake samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki na yankin. Ya ce, "ba ma kawai batun zaman lafiyar yankin yana da nasaba da aikin tsaron kasa ko na kare shi a fannin aikin soja ba, har ma yana shafar manyan tsare-tsare da manufofi masu gaskiya da ake tsarawa, ta yadda za a ba da tabbaci ga samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa harkokin zaman al'umma da tattalin arziki da bangarorin siyasa kamar yadda ya kamata. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yankin ya tanadi makudan kudade da ba a taba samun irinsa ba a da, ta haka an samar da kyakkyawar dama ga yankin wajen samun bunkasuwa mai dorewa. "


1 2 3