Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-20 15:16:35    
Titin al'adu na Nanxincang na Beijing

cri

Haka zalika kuma, akwai dakunan cin abinci na musamman fiye da goma a unguwar Nanxincang. Bisa dokokin da abin ya shafa da hukumar birnin Beijing ta gabatar, an ce, an haramta yin amfani da wuta kai tsaye a gine-ginen gargajiya, shi ya sa ake tafiyar da wadannan dakunan cin abinci a cikin gine-ginen da aka gina bisa salon gine-ginen gargajiya na kasar Sin. Saboda wadannan gine-gine na daura da dogayen rumbunan sarauta, shi ya sa suna da kyan gani, kuma suna da kyakkyawar kofa da wuraren cin abinci, su kan jawo masu sha'awar cin abinci, wadanda suke son cin abinci mai dandano, amma sun fi lura da wurin cin abinci. Malam Li Yang, darektan wani dakin cin abinci na unguwar Nanxincang, ya yi bayani kan dalilin da ya sa ya zabi wannan wuri, ya ce,

'Ina tafiyar da dakin cin abinci a cikin irin wannan wuri mai yanayin al'adu da tarihi, ba a iya samun sauran wurare kamar haka ba a duk kasar Sin. A zamanin da an ajiye hatsi a rumbuna, shi ya sa rumbuna alama ce ta girka hatsi. Dakin cin abinci wuri ne na cin abinci, mun dafa abinci a wurin ajiye abinci, dukan wuraren 2 na da nasaba da juna.'

Dakin cin abincin nan ba ma kawai ya samar da abinci irin na lardin Taiwan na kasar Sin ba, har ma ya samar da wasu abincin da a kan samar da su a gida kawai. Mai dakin cin abincin ya yi dabara ya sami izni daga wasu mashahuran mutane na rukunonin siyasa da wasannin motsa jiki da fasaha, ta haka a dakin cin abincinsa kawai ne ake dafa abinci bisa hanyoyin gargajiya da ake bi a cikin gidajen wadannan mutane. Ba a iya cin irin wadannan abinci a sauran dakunan ci abinci ba, shi ya sa in ku sami dama, to, ya fi kyau ku dandana kadan.(Tasallah)


1 2 3