Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-20 15:16:35    
Titin al'adu na Nanxincang na Beijing

cri

Rumbunan Nanxincang da ke gabashin birnin Beijing rumbunan sarauta ne inda aka soma ajiye hatsi yau da shekaru misalin dari 6 ke nan wato tun daga zamanin daular Ming da ta Qing, su ne tsoffin gine-gine da aka gina su a daidai lokacin da aka gina fadar sarakuna na kasar Sin wato Forbidden City, haka kuma, su tsoffin rumbunan sarauta ne mafi girma da ke nan sumuk garau a duk kasar Sin a yanzu. Yau rumbunan sarauta na da sun zama unguwar al'adu na zamani a duk birnin Beijing. A cikin shirinmu na yau za mu tabo magana kan sauye-sauyen rumbunan Nanxincang.

Unguwar Nanxincang mai al'adar musamman tana bakin wata muhimmiyar babbar hanyar zirga-zirga ta Beijing wato babban titin Ping'an, fadinta ya kai murabba'in mita dubbai, manyan gine-gine a nan su ne kattan rumbunan ajiye hatsi guda 9 masu dogon tarihi. Game da tarihin rumbunan Nanxincang, malam Zhao Zhiyi, wanda ke kula da wadannan rumbuna, ya fadi albarkacin bakinsa, ya ce,

'A can da rumbunan Nanxincang na dab da ganuwar birnin Beijing sosai, a lokacin can, wani kogi na gudu a kewayen ganuwar don tsaron Beijing, ya kuma hada hanyar ruwa ta Jinghang, wanda muhimmiyar hanya ce ta zirga-zirga kan ruwa a kasar Sin, ta haka an sami wani cikakken tsarin zirga-zirga kan ruwa. Dalilin da ya sa aka gina rumbunan Nanxincang a nan shi ne domin a sami sauki ne a fannin jigilar hatsi kan ruwa a tsakanin wannan wuri da hanyar ruwa ta Jinghang.'


1 2 3