Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-20 15:16:35    
Titin al'adu na Nanxincang na Beijing

cri

Malam Zhao ya kara da cewa, an yi ta ajiye hatsi a rumbunan Nanxincang har zuwa karshen zamanin daular Qing, wato a farkon karni na 20. Daga baya kuma, an ajiye makamai a nan saboda yake-yake. Bayan shekara ta 1949, wani kamfani ya ajiye kayayyakin masarufi a nan. Yanzu an sa wasu abubuwan zamani a rumbunan Nanxincang, gidajen baje kolin zane-zane na zamani da kungiyoyin rawar Latin da cibiyar faifai da dakunan cin abinci na musamman da kuma dakunan shan shayi na gargajiya da dai makamantansu da kuma rumbunan sarauta na zamanin da sun samar da tsarin gine-gine na musamman, wanda sabbi da tsoffi suke saje daidai da juna.

A cibiyar unguwar Nanxincang, wani rumbu, wanda ya fi daddewa kuma yana kasancewa cikin hali mafi kyau in an kwatanta ta da shi da sauran rumbunan, ya zama cibiyar samar da fai-fai da wurin jarrabawar kide-kide, sunanta kungiyar Yuefu. Wannan gini ya burge dukan wadanda suka shiga cikinsa. Kamfanin da ya yi hayar wannan rumbu ya yi amfani da kudin Sin yuan miliyoyi wajen yin kwaskwarima kan tsohon ginin a tsanake, bisa tushen girmama yadda yake a da. Bayan da masana masu ilmin gine-gine suka yi muhawara, kamfanin ya yi masa ado ba tare da yi masa barna ba, wato an iya cire dukan kayayyakin ado, ba a kawo wa tsohon ginin lahani ba, ta haka an ajiye abubuwa fasaha na sabon yayi a cikin wannan gini mai dogon tarihi. Wata jami'ar wannan kamfani madam Shao Donghong ta yi karin haske cewa,

'Ginin nan na da kyau sosai idan an kwatanta shi da sauran tsoffin fada na kasashen Turai. Muna ganin cewa, shi dukiya ne mai daraja kwarai. Idan ka sami wata dukiya, wajibi ne ka kiyaye ta yadda ya kamata, ka tono kyan ganinta.'


1 2 3