Kan mmuhimman batutuwa guda biyu da aka samu a Iraq a shekara bara wato mutuwar wani mudugu na kungiyar Al-qaeda Musab Al-zarqawi da tsohon shugaban kasar Iraq Saddam Hussein,ya ce da yake wadannan batutuwan guda biyu sun kawo tashe tashen hankula a wani lokaci,babu babban tasirin da za su jawo kan halin da ake ciki a Iraq.
Masani Yin Gang ya yi hasashen cewa hare hare na iya cigaba da faruwa a nan gaba a kasar Iraq,ana sa ran cewa al'amuran tsaro na kasar Iraq na nufi sassautawa tare da cigaba da ayyukan share fage a kewayen birnin Bagadaza da daidaita dabarun da za a yi.Ya ce "A ganina muhimmin abu wajen samu hali mai kyau a kasar Iraq shi ne ko za a iya tabbatar da sabbin manufofin siyasa na gwamnatin Iraq.haka kuma su dangana da cigaba da sojojin Iraq da na Amurka za su samu wajen murkushe dakaru masu tsatsauran ra'ayi.Idan ginshikan mabiya dariku masu tsatsauran ra'ayi da 'yan ta'adda na kungiyar Al-qaeda su sha kashi sosai,mutanen Iraq su farka daga tashe tashen hankulan 'yan darika,haka kuma shugabanni na mabiya dariku sun yi kira da a hada kai,al'amuran Iraq za su yiwu su samu cigaba mai faranta rai. 1 2 3
|