|

A ganin masani Yin Gang,tare da cigaba arangama tsakanin mabiya dariku,gwamnatin Iraq da dakarun kawance da Amurka ke jagora sun canza dabarun da suka yi amfani da su a da.Ya ce "Halin hadarin da Iraq ta shiga ciki ya jawo hankulan mahukuntan Iraq da dakarun hadin gwiwa,sai su dauki wasu matakai gwargwado.Da farko gwamnatin Iraq ta canza hanyoyin da ta bi a da wajen tafiyar da harkokin kasa,wato ta ki yarda da 'yan jam'iyyar Ba'ath ,musamman shugabanninsu da su shiga harkokin sake gina Iraq a fannin siyasa,ta kuma dauki hafsoshi na tsohuwar rundunar soja ta Iraq a matsayin saniyar ware.Ga shi yanzu ta yi watsi da wadnnan matakan da ta dauka a da kwata kwata,sai ba a sake ganin mabiya Saddam Hussein da ba a dauke su a matsayin da yadda ya kamata ba su shiga kungiyar Al-qaeda ko kungiyoyin yin adawa da dakarun Amurka ba.Ita ma Amurka ta canza dabaru nata wato ta fara yin shawarwari da dakaru masu adawa na Amurka.A sa'I daya gwamnatin Bush ta dauki mataki na tura karin sojojinta zuwa kasar Iraq.
Masani Yin Gang ya kuma dauka cewa wani abin da ya kamata a sa lura kan al'amuran kasar Iraq shi ne kasar Iran ta fito fili ta sa hannunta a ciki.Kan cigaban da aka samu dangane da batun nukiliya na Iran,Iran ta fara gane cewa shiga harkokin Iraq fiye da kima za ta yiwu janyo barna ga harkokin tsaronta.wannan yana nufin cewa sanya hannunta cikin harkokin Iraq bai zai haddasa ringima ga ga Amurka,akasin haka Amurka ta samu damar yin aron baki na kai mata hari,shi ya sa Iran ta fara daidaita dabarun nata.
1 2 3
|