Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-19 21:19:45    
Bayani kan harkokin Iraq

cri

Ran 20 ga watan Maris na bana,rana ce ta cikon shekaru hudu na yakin Iraq.Har wa yau dai mutanen kasar Iraq na ci gaba da arangama da zubar da jini da hawaye saboda wannan yakin da Amurka ta tayar kafin shekaru hudu da suka gabata.a cikin shekara guda ta baya.yanayin tsaro dake cikin kasar Iraq bai kai yadda ake bukata ba, ana ci gaba da samun tashe tashen hankula.Shehun mallami Yin Gang,masani na ofishin nazarin harkokin Asiya ta yamma da na Afrika na cibiyar nazarin ilimin zamantakewa ta kasar Sin ya yi bayani kan halin da ake cikin a kasar Iraq a shekarar bara.

A ganin masani Yin Gang,arangama da mabiya dariku daban daban suka yi na kara tsanani a shekarar bara a kasar Iraq,mabiya dariku na rukunoni daban daan su kan yi yaki da junansu.Ya ce "An samu sauye sauye a kasar Iraq a shekarar bara,wani abin sauyin da aka samu shi ne arangama tsakanin mabiyan dariku daban daban ta fara.Mun iya samo lokacin soma tabi na arangamar.A watan Fabrairu na shekarar bara ne bayan da kungiyar alqaeda ta wargaza wani muhimmin masallanci mai tsarki na Ali Al-hadi na mabiya darikar shi'ite da bom,masu tsatsauran ra'ayin dake cikin mabiya darikar Shi'ite sun kasa hakuri sun kai hare hare na ramuar gaya kan wasu masallantai da matsugunai na mabiya darikar Sunni,daga nan mabiya 'yan shi'ite da mabiyan 'yan Sunni sun yi yaki da juna.

A ganin masani Yin Gang,da akwai sabane sabane da ke tsakanin mabiya dariku kullum a kasar Iraq,duk da haka babu abun da ya janyo mummunar arangama tsakaninsu.amma an samu hare hare kan mabiyan 'yan darikar Shi'ite a kasar Iraq a cikin 'yan shekarun baya,alal misali,an kai hare hare da bom da kashe shugabanni na 'yan darikar Shi'ite,duk da haka 'yan shi'ite sun yi ayyuka tare da hikima,sun yi hakuri.Amma masallanci Ali Al-hadi,muhimmin masallanci mai tsarki ga mabiya 'yan shi'ite,yana da muhimmiyar ma'ama gare su.ta haka rushewar masallancin Al-hadi da bom ya kunna wutar yaki tsakanin mabiya dariku a kasar Iraq daga bisani.


1 2 3