Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-19 16:04:00    
Kwararru da masanan kasar Sin sun ba da shawarwari kan batun yawan mutane da bunkasuwar kasar

cri

Kuma kwararru da masana masu halartar taron sun ba da ra'ayoyinsu kan wasu matsalolin da ke kasancewa a fannin yawan matanen kasar Sin. Game da batun karuwar yawan tsofaffi, furfesa Wu Cangping da ke cibiyar nazarin yawan mutane da bunkasuwar kasa ta Jami'ar Jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa shekara ta 2020, yawan tsofaffin da shekarusu ya zarce 65 da haihuwa a kasar Sin zai kai miliyan 164, wato ya kai kashi 11.2 cikin dari na dukkan yawan mutanen Sin. Batun karuwar yawan tsofafi zai kara matsin lamba da za a yi wa tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwa da tsarin ba da hidima ga jama'a na kasar Sin. Yanzu tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar tsofafi na kauyukan kasar Sin ba shi da kyau, kuma samari masu dimbin yawa sun kwarara zuwa birane, sabo da haka za a tsananta halin da ake ciki wajen karuwar yawan tsofafi a kauyukan Sin.

Game da wannan, furfesa Wu ya ba da shawara cewa, ya kamata kasar Sin ta kyautata tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwa da tsarin ba da hidima ga tsofaffi nan da nan. A waje daya kuma ya kamata ta kyautata dokoki wajen kare hakkin tsofaffi da tallafa wa iyaye, da karfafa ayyukan ba da hidima ga tsofaffi na unguwanni, da kuma raya sana'o'in ba da hidima ga tsofaffi.

Jami'ai masu kula da ayyukan yawan mutane na kasar Sin sun saurari ra'ayoyin wadannan kwararru. Chen Li, shugaban sashen tsara shirin bunkasuwa na kwamitin kula da yawan matane da manufar yin haihuwa bisa tsari na kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ta ratsa ta matakai uku a fannin yawan mutane. Kuma ya kara da cewa,

"rage yawan haihuwa shi ne mataki na farko, kiyaye matsayin yawan haihuwa na kasa shi ne mataki na biyu wajen bunkasuwar yawan mutane. Yanzu ana shiga mataki na uku, wato warware batun yawan mutane ta tsararriyar hanya bisa tushen ci gaba da kiyaye karancin yawan haihuwa kamar yadda ya kamata. Ta hanyar kyautata ingancin mutane da kuma tsarin yawan mutane, za a iya canja kasar Sin daga wata kasa mai mutane da yawa zuwa wata kasar da ingancin mutanenta ke da kyau."(Kande Gao)


1 2 3