Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-19 16:04:00    
Kwararru da masanan kasar Sin sun ba da shawarwari kan batun yawan mutane da bunkasuwar kasar

cri

A cikin kasashe masu ci gaba da yawa, batun yawan matane shi ne ba a iya samun isassun masu aiki kamar yadda ya kamata ba. Amma batun da kasar Sin ta fuskanta ta sha bamban, sabo da an haifi jarirai masu matukar yawa kafin shekaru 70 na karnin da ya gabata, shi ya sa karuwar yawan haihuwa cikin sauri tana daya daga cikin kalubalen da kasar Sin ke fuskanta.

Kwararru suna ganin cewa, yanzu, yawan haihuwa na kasar Sin ya riga ya ragu zuwa wani matsayi na kasa. Dole ne a ci gaba da kiyaye irin wannan matsayi na kasa, amma ba a nufi cewa ba, karancin yawan haihuwa shi ne abu mafi kyau. Dailin da ya sa haka shi ne sabo da idan yawan haihuwa ya yi kasa kasa sosai, to zai tsananta halin da kasar Sin ke ciki wajen karuwar yawan tsofaffi, haka kuma zai kawo cikas ga kyautatuwar ingancin mutane, duk wadannan za su yi illa ga bunkasuwar zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasar Sin. Mr. Tian ya bayyana cewa,

"A idona, dole ne a kiyaye matsayin yawan haihuwa na kasa kamar yadda ya kamata. Kuma kiyaye matsayin yawan haihuwa na kasa ba ya nufin cewa, dole ne a tsaya tsayin daka kan haifuwa jariri ko jaririya daya tak a cikin ko wane gida ba. Ya kamata a dauki matakai bisa halin da kasar Sin ke ciki yanzu domin samun karancin yawan haihuwa kamar yadda ya kamata."


1 2 3