Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-19 16:04:00    
Kwararru da masanan kasar Sin sun ba da shawarwari kan batun yawan mutane da bunkasuwar kasar

cri

Kasar Sin wata kasa ce da ke da mutanenta mafi yawa a duk duniya. Domin sa kaimi ga bunkasuwar yawan mutane da tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin daidaici, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai masu yawa da kuma gabatar da manufofi a jere. Kuma abu mafi faranta rai shi ne, lokacin da aka tsara wadannan manufofi da matakai, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci kan saurarar ra'ayoyi da shawarwarin da kwararru da masana suka bayar. A gun taron kara wa juna ilmi da aka kira ba da jimawa ba kan yawan mutane da bunkasuwar kasar Sin, kwararru da masana masu yawa a fannin ilmin yawan mutane na kasar sun yi tattaunawa da mu'amala kan batutuwan da ke jawo hankulansu a fannin yawan mutane na kasar Sin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan taron kara wa juna ilmi.

Kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin haihuwa bisa tsari a shekaru 70 na karnin da ya gabata, kuma a cikin wadannan shekaru fiye da 30 da suka gabata, yawan jariran da aka haifa a kasar Sin yana ta samun raguwa, kuma jimlar ta ragu da kimanin miliyan 400. Game da wannan, kwararru sun bayyana cewa, ba a samu wannan sakamako mai kyau cikin sauki ba, amma yanzu ana bukata a ci gaba da nacewa ga bin matsayin karancin yawan haihuwa. Tian Xueyuan, manazarci na sashen yawan mutane na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin ya bayyana cewa,

"Mene ne dalilin da ya sa har yanzu ake mai da hankali kan rage yawan haihuwa a kasar Sin? Sabo da muhimmiyar matsala kan batun yawan mutane na kasar shi ne ana samun rarar masu aiki da yawa fiye da kima."


1 2 3