A gun taro kan aikin kudi na kasar Sin da aka kawo karshen lokacinsa ba da dadewa ba, an gabatar da cewa, za a yi kokari wajen bunkasa aikin ba da inshora ga aikin noma. Malam Wu Dingfu, shugaban hukumar kula da harkokin inshora ta kasar Sin ya bayyana cewa, a bana, za a gudanar da harkokin inshora ne musamman domin ba da taimako ga raya kauyuka da aikin noma. Ya ce, "a bana, za a gudanar da harkokin inshora musamman domin kauyuka da aikin noma da manoma. Na daya, za a nuna kwazo da himma wajen fitar da manufofi da abin ya shafa. Na biyu, za a yi kokari wajen gudanar da tsarin ba da inshora ga hasarar da ake sha daga wajen bala'i mai tsanani da ke shafar aikin noma. Na uku, za a sa kaimi ga kamfanonin inshora da su biya bukatu da manoma ke yi wajen ciyar da tsoffafi da kiwon lafiya da kuma raunuka da suke ji ba zato ba tsammani."
Aikin kudi da ake yi a kauyuka yana taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar aikin noma da tattalin arzikin kauyuka. Malam Xia Bin, shugaban sashen binciken aikin kudi na cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ce, bisa taimakon gwamnatin kasa ne, kauyukan kasar Sin za su kara samun taimakon kudi mai yawa, wannan yana kawo amfani ga kafa wani kyakkyawan tsarin aikin kudi a kauyukan. Ya bayyana cewa, "manufofi da gwamnatin kasar Sin ke dauka za su kara kyautata tsarin aikin kudi na kauyukan kasar, za a ba da taimako ga aikin noma a duk lokacin da ake yinsa, ta haka za a kara yawan kudi da manoma ke samu cikin sauri."(Halilu) 1 2 3
|