Amma abu mai faranta rai shi ne, bisa labarin da aka samu daga tarurruka kan aikin kudi da kasar Sin ta shirya a kwanakin nan, an sa ran alheri cewa, za a fara kawar da karancin kudi da ake yi a kauyuka. Gwamantin kasar Sin ta gabatar da cewa, za ta yi kwaskwarima a kan bankin aikin noma na kasar Sin daga duk fannoni, bayan haka bankin zai aiwatar da manufofinsa na ba da taimako wajen raya kauyuka da aikin noma da daga matsayin aikin kudi.
Shehun malami Lin Yifu, shugaban cibiyar binciken harkokin tattalin arzikin kasar Sin ta Jami'ar Beijing ya bayyana cewa, kauyukan kasar Sin za su kara samun kudade masu yawa ta hanyar yin kwarskwarima a kan bankin aikin noma na kasar. Ya ce, "manyan bankunan gwamnatin kasar Sin uku da ake kira cikin Ingilisanci kamar "Bank of China" da "Industrial and Commercial Bank of China" da kuma "China Construction Bank", dukanninsu suna gudanar da harkokinsu musamman domin ba da taimakonsu wajen raya birane da aikin masana'antu. A hakika dai, kauyukan kasar ma suna bukatar wani babban banki don ba da taimako ga raya aikin noma da kauyuka da kuma namoma."
Ban da bankin aikin noma na kasar, bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, banki mai suna "China Postal Savings" wanda ke da rassansa a ko ina cikin kauyukan kasar shi ma zai ba da kudin taimako don yin manyan ayyuka a kauyuka, da bauta wa manoma da kyau a fannin aikin kudi.
1 2 3
|