Matsayin aikin kudi ya yi kasa kasa a kauyukan kasar Sin, idan an kwatanta shi da na birane da garuruwanta wadanda ke bunkasa harkokin tattalin arzikinsu cikin sauri, sabo da haka ana fama da karancin kudi wajen raya kauyukan. A cikin irin wannan hali ne, gaggauta yin kwaskwarima a kan aikin kudi na kauyuka da kyautata tsarin aikin kudinsu sun zama manyan ayyukan tattalin arziki da ake yi bana a kasar Sin.
Tsarin aikin kudi na kauyukan kasar Sin yana baya-baya musamman a fannoni kamar, rassan da manyan bankunan kasuwancin kasar suka kafa a kauyuka ba su da yawa, a halin yanzu, ban da cewar bankin aikin noma na kasar Sin na gudanar da harkokinsa a kauyuka, sauran manyan bankunan gwamnatin kasar ba su yin haka, sabo da haka ana fama da karancin kudi sosai wajen raya kauyukan. Ban da wannan kuma, irin inshora da ake bayarwa a kan aikin noma ma kalilan ne.
1 2 3
|