Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 15:47:40    
Wani bayani dangane da Takaitaccen tarihi na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Bisa babban tsarin Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, an ce, hakkin kwamitin duk kasa da na wuri wuri su ne kamar haka: Na farko, na da ikon jefa kuri'a da ikon zabe da ikon a zabe shi a gun taron da aka yi. Ha biyu, na da ikon ba da shawara da kai suka a kan ayyukan taron da aka yi. Na uku, na da ikon shiga tattaunawa kan babbar manufar kasa da manyan al'amuran wurin a gun taron da aka yi. Na hudu, na da ikon ba da shawara da kai suka kan ayyukan da hukumomin kasa da ma'aikatan kasa suka yi. Na biyar, na da ikon tono ayyukan da suke saba da dokokin shari'a da shiga cikin ayyukan bincike da sa ido. Na shida, na da yancin ba da shelar janye jiki daga Majalisar. Na Bakwai, a lokacin da aka bayar da gargadi ko soke cancantar matsayin shiga Majalisar, in ba a amince da wannan ba, to za a iya samun ikon ba da rokon sake bincike a kai.

Dawaniyoyin sa kai da ke bisa wuyan mambobin Majalisar su ne, na farko, amincewa da babban tsarin Majalisar da aiwatar da shi, Na biyu , amincewa da aiwatar da kudurin taron kwamitin din din din da na taron duk kwaminitocin wurin, Na uku, mambobin Majalisar na wuri wuri ya kamata su aiwatar kuma su amince da kudurin duk kasa da na dukan wuri wuri.(Halima)


1 2 3