Bin hanyar zabe da jefa kuri'u don aiwatar da harkokin mulki da kuma yin shawarwari sosai da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a kafin zabenta da jefa kuri'u, hanyoyi ne guda biyu masu muhimmanci sosai ga aiwatar da dimokuradiyar gurguzu ta kasar Sin. Huldar da ke tsakanin bangarori uku wato Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da gwamnati ita ce kamar haka: Na farko, yin shawarwari sosai kafin tsai da kuduri , na biyu, yin shawarwari sosai bayan tsai da kuduri, na uku, aiwatar da ayyuka bayan tsai da kuduri, a karkahsin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ne dukkan bangarori uku suke aikinsu na kansu cikin hadin guiwa, kuma suna samar wa juna karin taimako da cim ma burinsu na kansu. Wannan ne tsarin siyasa da ya dace da halin da kasar Sin take ciki da halayen musamman na kasar Sin .
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa tana kunshe da Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da rukunonin dimokuradiya da jam'iyyun dimokuradiya daban daban da mutanen da ba su cikin kowace kungiya da rukunonin jama'a da wakilan kananan kabilu daban daban da na rukunoni daban daban da 'yanuwan yankin musamman na Hongkong da na Macao da na Taiwan da wakilan Sinawan da suke zama a kasashen ketare da sauran mutanen da aka ba su gayyata ta musamman.
1 2 3
|