Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 15:47:40    
Wani bayani dangane da Takaitaccen tarihi na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Yawan wa'adin aikin Majalisar ya kai shekaru biyar, Majalisar yanzu ita ce ta 10. Kwamitin duk kasa ya kafa kujeru na shugaba da na mataimakan shugabanni da yawa da na babban sakatare .

Kwamitin din din din na Majalisar duk kasa ne ke shugabantar ayyuka na yau da kullum.

Kwamitin duk kasa ya kafa kwaminitocin musamman da yawa da sauran hukumomin aiki.

Kwamitin duk kasa na goma na Majalisar ya kafa kwamitin ba da shawara da kwamitin tattalin arziki da kwaminitocin musamman guda 9 da dai saruansu.

Ta wace hanya ce ake zaben mambobin Majalisar?

Da farko, an gabatar da shawara ga zaben wadanda ake so. Mambobin kwamitin duk kasa da aka ba da shawarar zabensu ta hanyar shawarwari suna kunshe da kwamitin tsakiya na jam'Iyyu daban daban da rukunonin jama'a daban daban da mutanen da ba su cikin kowace kungiya da dai sauransu.

Sa'anan kuma, sassan da abin ya shafa na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun kirawo sassan da abin ya shafa na Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa don yin shawarwari a tsakaninsu, sa'anan kuma sun tsai da sunayen mambobin, sa'anan kuma an gabatar da wadannan sunaye ga taron kwamitin din din din don raba gardama ta hanyar shawarwari, sai kuma za a sami amincewa daga wajen mambobin kwamitin din din din da yawansu ya wuce rabi .


1 2 3