Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-22 20:33:09    
Kasar Birtaniya za ta janye wasu sojoji daga kasar Iraq

cri

Na biyu kuma, saboda sojojin kasar Birtaniya suna tafiyar da ayyuka a kasashen Iraq da Afghanistan a lokaci daya, shi ya sa suna fuskantar mawuyancin hali na raguwar karfi da yin karancin makamai a yanzu. A cikin irin wannan hali ne, Mr. Blair ya sanar da janye wasu sojoji daga kasar Iraq, wannan ya nuna cewa, yana yunkurin fitar da sojojin kasar Birtaniya daga lakar yakin kasar Iraq.

Kafin ya sanar da janye wasu sojojin kasar Birtaniya daga kasar Iraq a ran 21 ga wata, Mr. Blair ya yi tattaunawa sosai da muhimmiyar kawanyarta wato kasar Amurka kan batun janye sojoji. Kakakin fadar gwamnatin kasar Amurka wato White House ya bayyana cewa, shugaba Bush ya tattauna shirin janye sojojin Birtaniya daga kasar Iraq tare da Mr. Blair a ran 20 ga wata, shirin da gwamnatin Birtaniya ta tsara game da rage yawan sojojinta a kasar Iraq ya nuna cewa, rundunar sojan kasar Birtaniya ta riga ta kammala wasu ayyukanta a kudancin kasar Iraq.

Shugaban jam'iyyar Conservative ta kasar Birtaniya David Cameron ya bayyana cewa, jam'iyyarsa ta yi maraba da kudurin janye sojoji da gwamnatin da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwadago ta yi, amma batutuwan da ake bukatar daidaita su a yanzu su ne ko sojojin Iraq suna iya kiyaye kwanciyar hankali a kudancin kasar ko a'a, sa'an nan kuma, ko sauran sojojin Birtaniya a kasar Iraq suna iya kiyaye kansu daga hare-haren da dakarun da ke adawa da gwamnatin suka yi ko a'a.(Tasallah)


1 2 3