Masu kula da harkokin yau da kullum sun nuna cewa, a matsayinsa na kawancen kasar Amurka mafi muhimmanci, Mr. Blair ba yadda zai yi ba, sai ya yanke shawarar janye wasu sojoji daga kasar Iraq.
Da farko, a fannin siyasa a gida, Mr. Blair ya yi ta samun zargi daga akasarin ra'ayoyin jama'a a gida kan batun kasar Iraq, ya kuma biya da yawa a fannin siyasa a sakamakon haka. Tun bayan da kasashen Birtaniya da Amurka suka ta da yakin kasar Iraq a shekara ta 2003 har zuwa yanzu, yawan mutanen da suke goyon bayan Mr. Blair sai raguwa yake yi sosai, haka kuma, 'yan jam'iyyar kwadago da ke karkashin shugabancinsa sun yunkura tube shi daga kan mukaminsa sau da yawa. A watan Mayu na shekarar nan, za a yi zabubbuka a kananan hukumomin kasar Birtaniya, kuma Mr. Blair zai mika mukaminsa a shekarar bana. Shi ya sa dalilin da ya sa Mr. Blair ya sanar da janye sojoji daga kasar Iraq shi ne domin kyautata mummunan halin da jam'iyyar kwadago ke ciki. Bisa halin da ake ciki a yanzu, matakin da Mr. Blair ya dauka zai kawo alheri ne ga zabubbukan da za a yi a kananan hukumomin kasar nan da watanni 3 masu zuwa, da kuma shi kansa, wanda ya yi shekaru 10 yana mulkin kasar Birtaniya a matsayin firayim minista.
1 2 3
|