Ran 21 ga wata, a gaban 'yan majalisar wakilai ta kasar Birtaniya, firayim ministan kasar Tony Blair ya sanar da cewa, gwamnatin Birtaniya ta yi niyyar rage yawan sojojinta a kasar Iraq zuwa 5500 nan da watanni da dama masu zuwa, a maimakon sojoji 7100 na yanzu, wato ke nan za ta janye misalin rubu'in sojojinta da take girke a kasar Iraq.
Mr. Blair ya sanar da wannan kuduri ne a gabannin ranar cikon shekaru 4 da kasashen Birtaniya da Amurka suka tura sojoji zuwa kasar Iraq. Mr. Blair ya bayyana cewa, yanzu halin da ake ciki a wuraren da ke kusa da birnin Basra na kudancin kasar Iraq ya sha bamban da na birnin Bagadaza sosai, a galibi dai an tabbatar da kwanciyar hankali a kudancin kasar. Ran 20 ga wata, rundunar sojan kasar Birtaniya a kasar Iraq ta mika karagar mulkin birnin Basra ga takwaranta na kasar Iraq, yanzu sojojin kasar Iraq sun iya tabbatar da tsaron kai a wurin, shi ya sa wasu sojojin Birtaniya za su iya janye jikinsu. Mr. Blair ya kara da cewa, gwamnatinsa ta dauki wannan mataki ne don nuna wa 'yan kasar Iraq cewa, kasar Birtaniya da sauran kasashen da suke girke sojoji a kasar Iraq ba su yi niyyar wuce wa'adin da ya wajaba ga girke sojojinsu a wannan kasa. Amma a sa'i daya kuma, ya yi bayanin cewa, mai yiwuwa ne sojojin kasar Birtaniya za su ci gaba da zauna a kasar Iraq har zuwa shekara ta 2008 don taimakawa wajen horar da sojojin kasar Iraq da ba su tallafawa da kuma kiyaye hanyoyin zirga-zirga da bakin iyakar kasa a nan.
1 2 3
|