Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:21:49    
Wurare daban daban na kasar Sin sun shirya shagulgulan al'adu iri iri da yawa don murnar bikin yanayin bazara

cri

A birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin, shagulgulan murnar bikin yanayin bazara da aka shriya suna da halayen musamman sosai na wurin. Lardin Sichuan ya yi suna sosai bisa sanadiyar samun abinci mai dadin ci sosai tare da albarkattun halittu da yawa wajen yin yawon shakatawa. A birnin Chengdu, daga ranar 16 ga wannann wata ana soma shirya kasaitattun tarurukan haihali a wuraren yawon shakatawa, ana kara wadatar da jama'a wajen zaman rayuwarsu a bikin yanayin bazara ta hanyar nuna wasannin tunawa da kakani-kakaninsu da yin nunin kayayyakin al'adar jama'a da shirya yawon shakatawa a zagaye da samar da abinci mai dadi iri iri da dai sauransu. Wata malama mai kula da ayyukan shirya shagulgulan kuma mai suna He Hongying ta bayyana cewa, mun shirya wasannin fasaha iri iri da yawa don murnar bikin yanayin bazara, ciki har da wasannin kundumbala da wasan wake-wake da raye-raye da dai sauransu, wasu ma sauran mutane ba su iya yin su ba, dukkansu sun bayyana halayen musamman na al'adunmu, a sa'I daya kuma, muna shirya wasu gasanni a tsakanin wasu kwararru, wato wasan Kongfu da wasan mutum mutumi da dai sauransu.

A lardin Yunan da ke kudancin kasar Sin, dayake kananan kabilu da yawa suna zama a nan a cunkushe, shi ya sa al'adunsu da al'adarsu na gargajiya sun sami karbuwa sosai daga wajen mutanen gida da na waje da yawan gaske, a tsohon birnin Xi'an da ke arewa maso yammacin kasar Sin, an shirya nunin hotunan kayayyakin tarihi masu daraja sosai da kuma tattara takardun musamman da a kan manna a kan gefunan kofa don isar da sakon fatan alheri a lokacin bikin yanayin bazara, wadannan aikace-aikace sun sami maraba sosai daga wajen jama'ar birnin. (Halima)


1 2 3